Barin AC Milan ya zamo min alheri.

Alexandre Pato
Image caption Pato yace nayi farinciki lokacin da Brazil ta gayyace ni na buga mata wasa.

Tsohon dan wasan AC Milan Alexandre Pato ya ce komawarsa Corinthians ta zamo masa alheri.

Dan wasan mai shekaru 24, na daya daga cikin yan wasan da suka jefa wa Brazil kwallaye shida da nema.

A lokacin da suka kara a wasan sada zumunci da Australia ranar Asabar.

Pato wanda ya koma kungiyar a watan Janairu ya ce barin AC Milan ya ba shi damar buga wasa a kai a kai.

Har ma Brazil ta gayyace shi ya buga mata wasa.

Brazil zata kara da kasar Portugal ranar Talata a wasan sada zumunci.