Mun sayi Etoo ne a madadin Rooney

Samuel Eto'o
Image caption Chelsea zata samu gogayya a 'yan wasanta masu jefa kwallo a raga

Jami’in Chelsea, Michael Emenalo, ya ce sun sayi Samuel Eto’o a rashin sayen Rooney daga Manchester United.

Emenalo ya ce Samuel Eto’o kwararren dan wasa ne da kungiyar za ta dogara da shi domin samun sakamakon wasa.

Ya ce kungiyar tana da Romelu Lukaku mai shekaru 20, to amma tana kokarin samun gogaggun 'yan wasan gaba.

Chelsea ta dauko Samuel Eto'o daga kungiyar Anzi Makhachkala, koda yake kungiyar tana da ’yan wasa masu zura kwallo a raga da suka hada da Fernando Torres da Demba Ba.

Karin bayani