Zidane ya jinjinawa Lampard

Image caption Zidane da Lampard suna taka leda

Gawurtaccen dan kwallon Faransa, Zinedine Zidane ya ce dan wasan Ingila, Frank Lampard ne kashin bayan tawagar duk da cewar yana da shekarun haihuwa 35.

Dan kwallon Chelsea din, na shirin bugawa Ingila kwallo a karo na 100, idan tawagar ta hadu da Ukraine a Kiev a ranar Talata.

Zidane ya shaidawa BBC cewar " dan wasa ne da ya ciri tura, Lampard shugaba ne".

Zidane wanda shine mataimakin koci kuma Darektan Wasanni a Real Madrid, ya ce Ingila za ta tsallake zuwa gasar kofin duniya da za ayi a Brazil a shekara ta 2014.

Zidane ya bugawa Faransa kwallo a wasanni 108 inda ya zira kwallaye 31.

Karin bayani