Aboutrika ya buga wa Masar wasa 100

Mohamed Aboutrika na kungiyar kwallon kafa ta Al-ahly
Image caption Masar ta matsa wa Guinea lamba a sulusin karshe na wasan

Mohamed Aboutrika ya zamo dan wasa na 9 da ya bugawa Masar wasanni 100, bayan da kasar ta kara da Guinea.

Masar ta doke Guinea da ci 4-2, abin da ya kawo karshen wasannin cancantar shiga gasar cin kofin duniya na rukuninsu.

Tuni da ma Masar din ta samu nasara a rukunin C, inda ta kai zagayen karshe na wasan kifa daya kwala, na gasar cin kofin kwallon duniya da za a yi a Brazil a badi.

Amma kasar Guinea wacce ita ce ta biyu a rukunin, ta shiga gaba ne cikin mituna hudu da soma wasan, bayan dan Masar Adam El Abd ya ci gidansu.

Sakamakon wasan dai ya sa Masar ta zamo kasar Afrika tilo, da ta kammala wasan rukuni da maki 18.