Nadal ya lashe gasar tennis ta US open

rafael Nadal
Image caption Nadal ya dauki kofuna a gasa 13 kenan

Shahararren dan wasan tennis din nan Rafael Nadal ya doke Novak Djokovic, abin da ya kai shi ga lashe gasar US Open.

Dan wasan dan Sapaniya ya samu nasara ne da ci 6-2 3-6 6-4 da kuma 6-1 a karawar da suka yi a New York, kuma hakan ya bashi nasarar daukar kofi a karo na biyu a gasar.

A bara Nadal bai samu shiga gasar ba saboda jinyar kaurinsa da ya yi na tsawon watanni bakwai, yanzu ya komo fagen fama, domin karbe matsayinsa na daya.

"Wannan gagarumar nasarar na da ban mamaki" Inji Rafael. "Ban taba zato ba, rayuwa kenan kuma na yi sa a game da abin da nake samu."