Bale zai buga wa Real wasan farko

Image caption Gareth Bale

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti, ya ce dan kwallon da yafi kowanne tsada a duniya Gareth Bale zai buga wasansa na farko a kungiyar idan ta hadu da Villareal a ranar Asabar.

Dan shekaru 24, Bale ya koma Real daga Tottenham a kan fan miliyan 85.3 a ranar daya ga watan Satumba, kuma kawo yanzu bai buga wasa minti 90 ba a kakar wasa ta bana saboda ciwon kafa.

Ancelotti yace " Bale zai buga wasan, amma banda tabbas ko za a fara dashi ko kuma zai zauna a benci".

Yadda aka sayi Bale ya zarta kudin da aka sayi Cristiano Ronaldo daga Manchester United a shekara ta 2009 a kan fan miliyan 80.

Real ta samu nasara a wasanninta uku a jere a gasar La Liga ta bana, sannan a ranar Talata za ta kara da Galatasaray a gasar zakarun Turai.

Karin bayani