Da na tsani Mourinho —Eto'o

Image caption Eto'o ya ce akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da Mourinho.

Dan wasan gaba na Chelsea, Samuel Eto'o, ya bayyana cewa koda yake yanzu akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da Kocin kungiyar, Jose Mourinho, amma a da sun tsani juna.

Dan wasan mai shekaru 32 a duniya ya ce Mourinho ne ya yi sanadiyar komawarsa Chelsea bayan su biyun sun hada hannu wajen ganin sun lashe Gasar Zakarun Turai a shekarar 2010 lokacin suna Inter Milan.

Eto'o ya shaidawa BBC cewa ba koda yaushe ne shi da Mourinho ke jituwa ba.

Ya ce:"Dangantakar da ke tsakanina da Jose tana da ban sha'awa. Da farko, mun tsani juna amma a hankali muka rika kaunar juna''.

Eto'o dai ya sanya hannu kan kwantaragin shekara daya a Chelsea, bayan da ya bar kungiyar kasar Rasha Anzhi Makhachkala a matsayin aro.

Karin bayani