Qatar ta yi watsi da suka kan gasar 2022

Hassan al-Thawadi
Image caption Al-Thawadi ya shaida wa BBC cewa, Qatar ta yi aiki tukuru domin cimma dokokin daukar nauyin gasar

Shugaban shirya wasannin cin kofin kwallo na duniya ta shekarar 2022 na Qatar, ya yi watsi na kiran da wasu ke yi na a baiwa wata kasa daukar nauyin gasar.

Ana tsammanin hukumar kwallo ta duniya FIFA, za ta dauke wasan zuwa lokacin sanyi, domin kaucewa tsananin yanayin zafi na Qatar.

Shugaban kungiyar kwallon kafa, Greg Dyke ya ce akwai yiwuwar a dauke gasar, idan an kasa cimma matsaya game da lokacin da ya dace a yi wasannin a Qatar.

Sai dai Hassan al-Thawadi ya dage cewa, babu wata hujja da za ta sa a dauke wasan na shekarar 2022 daga Qatar kamar yadda aka shirya.