Coutinho zai yi jinya makwanni 6

Image caption Philippe Coutinho

Dan kwallon Liverpool Philippe Coutinho, zai yi jinya na raunin da ya samu a kafada, ba zai sami buga wasa ba har karshen watan Oktoba, kamar yadda kungiyar ta sanar.

Coutinho dan kasar Brazil mai shekaru 21 da aka sayo daga Inter Milan kan kudi kimanin fan miliyon takwas a watan Janairu, ya taimakawa Liverpool darewa matsayi na daya a gasar Premier ta Ingila bayan wasanni hudu.

Ko da yake Luis Suarez baya bugawa liverpool wasa, bisa dakatar dashi wasanni goma bayan da aka sameshi da cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic a kakar wasa ta bara, kungiyar ta fara wasa da kafar dama inda ta samu nasara akan Stoke da Aston Villa da Manchester United da kuma canjaras da Swansea a ranar Litinin data gabata.

Daniel Sturridge ya zamo dan wasan Ingila na farko daya zurawa Liverpool kwallaye a wasannin ta hudu data buga a gasar Premier ta bana, yayinda Suarez zai dawo wasa a league kof da zasu kara da Manchester United ranar 25 ga watan Satumba.

Karin bayani