Manchester United ta ci riba

Image caption Manchester United

Zakaran gasar Premier ta Ingila, Manchester United ta bayyana samun karin kudin shiga na fan miliyan 363 cikin watanni 12 har zuwa watan Yuni.

Kungiyar wacce iyalan Glazer ke jagoranta, ta samu karin kudaden haraji ne daga tallar da take samu.

Ta samu ribar fan miliyan 146.

Daga cikin tallar da United ta samu a shekarar da ta wuce hadda na batun tallar mota kirar Chevrolet a gaban riga a kakar wasan da ta wuce.

Da kuma tallace-tallace a talabijin na kusan fan miliyan 102.

Karin bayani