Laifi na ne da aka doke mu- Mourinho

Image caption Jose Mourinho

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce laifinsa da kungiyarsa ta sha kashi a wajen Basel da biyu da daya a wasam zakarun Turai.

Oscar ne ya soma zira kwallo kafin Mohamed Salah ya farkewa Basel daga bisani kuma Marco Streller ya ci musu kwallo ta biyu.

Mourinho yace " idan muka fuskanci rashin nasara, bana maganar 'yan wasa, ina daukar alhakin haka".

Sabon dan wasan Chelsea Samuel Eto'o da Demba Ba sun buga wasan, a yayinda Fernando Torres bai buga ba.

Amma dai Mourinho ya ce babu matsala duk da cewar 'yan wasansa na gaba basa iya zira kwallo.

Karin bayani