Ozil ya yi sanadiyar lallasa Stoke

Metsul Ozil
Image caption Sakamako na nuna yadda Ramsey da Ozil, suka zamo kashin bayan sauya wasanmu, in ji Wenger

Mesut Ozil na da hannu wajen doke Stoke city a dukkan kwallaye uku da Arsenal ta zura musu a raga.

Aaron Ramsey shi ya fara zura kwallo bayan mai tsaron gida, Asmir Begovic, ya kare dukan falan-dayan da Ozil ya buga masa.

Stoke ta farke kwallonta ta hannun Geoff Cameron kafin a tafi hutun rabin lokaci, bayan Marko Arnautovic ya buga kwallo ta doki turke.

Per Mertesacker da Bacary Sagna ne suka zura kwallayen da Ozil ya saka musu, lamarin da ya bai wa Arsenal damar darewa kan teburin Gasar Premier.