Arsenal ta samu riba saboda Van Persie

Filin wasa na Arsenal
Image caption Arsenal ta ce tana shirin sayen sabbin 'yan wasa a bana

Ribar Arsenal ta ragu daga kimanin fam miliyan 36 zuwa fam miliyan 6, duk da cewa kulob din ya samu fam miliyan 47 daga sayar da Robin Van Persie da Alex Song.

Sayar da 'yan wasan biyu ya hana Arsenal yin asara a wannan shekarar zuwa karshen watan Mayu, kungiyar ta kare kakar wasannin bara babu kofi.

Arsenal wanda shahararren mai kudin nan Stan Kroenke ya mallaki mafi yawan hannun jarinta, ta sayar da Van Persie ga abokiyar hamayyarta Manchester United.

Arsenal ta sami gurbin gasar kofin zakaru ta nahiyar Turai, ta kuma fara gasar Premier ta bana da kafar dama a matsayi na daya.