Walcott zai yi jinyar makwanni

Image caption Theo Walcott

Theo Walcott ba zai sami damar buga wasan neman gurbin kofin duniya da England za ta kara da Montenegro da Poland, sakamakon aiki da za'a yi masa a mararsa.

Walcott mai shekaru 24, bai sami karawa da Arsenal tayi da Stoke City ranar Lahadi duk da cewa Arsenal ta fitar da sunan sa a yan wasan da zasu buga mata kwallo.

"Theo zai yi jinya na satuttuka ," inji kocin Arsenal Arsène Wenger.

"Ya gamu da rauni a kasan mararsa, kuma ba kaba bace, amma yar matsala ce a mararsa."

Karin bayani