Barcelona na hangen 'yan Chelsea 3

kocin Chelsea Jose Mourinho
Image caption Yan wasan uku basa samin buga wasa a kai a kai

Barcelona na sanya idanu kan 'yan wasan Chelsea, Juan Mata da Fernando Torres da Cesar Azpilicueta

'Yan wasan uku sun gaza yin wasa a kai a kai tare da koci Jose Mourinho, lamarin da ya sa ake hasashen makomarsu a Stamford Bridge.

Branislav Ivanovic ya maye gurbin Azpilicueta, yayin da Mourinho ya zabi Samuel Eto'o maimakon Fernando Torres.

Tun a farko tsohon kocin Real Madrid ya bukaci Juan Mata cewa ya koma wasan gefe, tunda ya zabi Oscar a dan wasansa lamba 10.