Lewandowski zai koma Munich

Roberto Lewandoski
Image caption Tun a kakar wasa ta bara dan wasan yaso komawa Bayern Munich

Dan wasan Borussia Dortmund Roberto Lewandoski ya ba da tabbacin zai koma Bayern Munich shekara mai zuwa

Lewandoski, mai shekaru 25, kwantiraginsa zai kare a watan Janairu, ya na kuma fatan komawa Munich, lokacin da za a bude kasuwar sayen 'yan wasa a bazara.

Dan wasan ya zura kwallaye 36 a kakar wasa ta bara.

Mario Gotze ya koma Munich daga Dortmund a lokacin hunturu kan kudi kimanin fan miliyon 31.