Arsenal za ta kara da Chelsea

'Yan wasan kulob din Arsenal
Image caption Arsenal ta dauki kofin gasar a shekarar 2005, yayin da Chelsea ta dauka a shekarar 2007

Kulob din Arsenal zai dauki bakuncin Chelsea, a zagaye na hudu na gasar cin kofin Capital One.

Nasarar da Manchester United ta samu na doke Liverpool ci 1-0, ya sa za ta dauki bakuncin Norwich, yayin da Newcastle za ta kece raini da Manchester City.

Ita kuwa Birmingham City za ta fafata ne a gida da Stoke, kulob din Tottenham zai kara da Hull, sai Sunderland da za ta hadu da Southampton.

Za a buga wasannin ne a ranar 29 ko 30 ga watan Oktoba mai kamawa.