Brazil da Spain a kwallon rairayi

Brazil zata kara da Spain a wasan kusa dana karshe
Image caption Za a buga wasan kusa dana karshe ranar Asabar a filin wasa na Tahua To'ata Beach da ke Tahiti.

Brazil ta kai wasan kusa dana karshe bayan da ta yi nasara a kan Japan da ci 4 - 3, a Gasar Kofin Duniya ta kwallon rairayi da Tahiti ke karbar bakunci.

Brazil za ta kara da Spain, yayin da Spain ta kai wasan kusa dana karshe bayan da ta samu nasara a kan El- Salvador da ci 2-1.

Mai masaukin baki, Tahiti za ta kara da Rasha, bayan da ta sami nasara a kan Argentina da ci 6-1.

Ita kuwa Rasha ta yi nasara a kan Iran da ci 6-5 a wasannin da aka kara a yau.