Suarez zai yi iya kokarinsa a Liverpool

Luis Suarez
Image caption Rabon Suarez da buga kwallo tun ranar 22 ga watan Aprilu

Dan wasan gaba na kulob din Liverpool, Luis Suarez ya ce zai yi wasa tukuru ga kulob din, a taka ledarsa ta farko bayan ya dawo fagen tamaula.

An haramtawa Suarez dan Uraguay mai shekaru 26 yin wasanni goma, bayan ya ciji Branislav Ivanovic dan wasan Chelsea.

Suarez ya nemi ya bar Liverpool, amma kulob din ya ki sayar da shi.

Dan wasan wanda ya yi wasa na tsawon mintoci 90, a karawar da kulob dinsa ya yi da Manchester United ya ce "Sakamakon bai yi kyau ba saboda an doke mu, amma mun yi wasa mai kyau, mun samu dama kuma mun barar da su."