'Ina son Wenger ya dade a Arsenal'

Image caption Mai kulob din Arsenal, Stan Kroenke

Mai kulob din Arsenal, Stan Kroenke ya ce yana alfahari da manajan kungiyar, Arsene Wenger kuma yanason manajan ya kara dadewa a kulob din.

Wenger wanda ya shafe shekaru 17 yana jan ragamar Gunners, yana kakar wasansa ta karshe a Emirates.

Da aka tambayeshi ko Wenger na cikin shirinsu a nan gaba, Kroenke sai ya shaidawa jaridar Daily Telegraph cewar "tabbas haka lamarin yake".

Wenger na shan suka daga wajen magoya bayan Arsenal a kan cewar baya sayen manyan 'yan wasa kuma an shafe shekaru kusan takwas ba tare da lashe kofi ba.

Sai dai Wenger din ya nuna cewar Arsenal za ta nemi lashe kofi a kakar wasa ta bana, inda kungiyar ta sayi dan kwallon Jamus, Mesut Ozil a kan fiye da fan miliyan 42.

Karin bayani