Jordan ya zama shugaban FA

Danny jordan shugaban fa ta Afirka ta kudu
Image caption Jordan ya yi nasara a zaben da suka fafata da yan takara biyu

Danny Jordan ya lashe kujerar shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika ta Kudu.

Sabon shugaban ya taka rawa gagarima lokacin da kasarsa ta karbi bakuncin gasar Kofin Duniya, hakan ya sa ya ci zaben.

Jordan ya samu kuri'a 162 shi kuma Mandla Mazbuko ya sami kuri'a 88.

Tsohon shugaban hukumar kwallon Kirsten Nematandani bai sami kuri'a ko daya ba.