Messi zai yi jiyyar sati uku

Lionel Messi Argentina
Image caption Messi yayi fama da rauni a karshen kakar bara

Dan wasan Barcelona Lionel Messi, zai yi jinya ta sati uku, saboda raunin da ya ji a cinyarsa.

Messi dan kasar Argentina ya samu raunin ne lokacin da kungiyarsa ta samu nasara da ci biyu da nema akan Almeria a ranar Asabar da ta gabata.

Saboda raunin da ya samu ba zai samu damar buga wasan kofin Zakarun Turai da za su kara da Celtic ranar Talata ba.

Wannan raunin shi ne na biyu da Messi ya ji, tun a farkon kakar wasa ta bana ya yi jinya lokacin da ya kuje a cin yarsa.

Haka kuma Messin ba zai buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Valladolid da kuma Osasuna a gasar La-Liga ba.