Mancini ya zama sabon kocin Galatasaray

Image caption Mancini ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasary ta dauki Roberto Mancini a matsayin sabon kocinta.

Mancini, tsohon kocin Manchester City, ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru 3 a kungiyar.

A baya dai, kungiyar ta sanar cewa Mancini yana tattaunawa da mahukuntanta domin yiwuwar komawarsa can.

Mancini ya maye gurbin Fatih Terim ne, wanda aka kora a makon jiya.

Manchester City ta kori Mancini a watan Mayu, duk da ya lashe kofin Premier.

Karin bayani