Galatasaray na tattaunawa da Mancini

Image caption Roberto Mancini

Roberto Mancini na tattaunawa da zakarun kwallon Turkiya Galatasaray a yinkurin nada shi manajan kulob din.

Kungiyar ta bayyana a shafinta na Twitter cewar Mancini ya gana da darektocin kulob din.

Dan kasar Italiyan zai maye gurbin Fatih Terim ne wanda aka kora a makon da ya gabata saboda rashin jituwa a kan batun sabuwar yarjejeniya.

Manchester City ta kori Mancini a watan Mayu, shekara daya tal bayanda ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar Premier.

Mancini ya lashe gasar Italiya sau uku tare da Inter Milan kafin ya lashe kofin Premier a Ingila dana FA tare da Manchester City.

Karin bayani