'Na zaci Suarez zai bar Liverpool'

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard, ya ce ya yi fargabar dan wasansu Luis Suarez zai bar kulob din.

Suarez mai shekaru 26, ya bayyana aniyarsa ta barin Anfield bayan Arsenal da Real Madrid sun yi zawarcinsa.

Gerrard yace" idan kana da babban dan wasa kamar Suarez, tabbas kungiyoyi za su dinga kai masa cafa".

Gerrard mai shekaru 33, ya kara cewar, a duk safiya idan ya wayi gari sai ya dinga tunanin dan kwallon zai tafi.

Suarez ya koma fagen tamaula a Liverpool, bayan dakarwar wasanni 10 da aka yi masa sakamakon cizon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic.

Karin bayani