Ghana ta gayyaci Richard Kingson

Image caption Golan Ghana, Richard Kingson

Ghana ta gayyaci mai tsaron gida Richard Kingson cikin tawagar 'yan kwallo 25 da za su fuskanci Masar a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014.

Kingson mai shekaru 35, ya koma cikin tawagar Black Stars bayan shafe shekaru biyu ba a gayyatarsa, inda kuma aka kira Sulley Muntari, Jordan Ayew da kuma Jerry Akaminko.

Kocin Black Stars Kwesi Appiah ya gayyanci gogaggun 'yan wasan don fafatawa a wasan mai mahimanci a birnin Kumasi.

Tawagar Ghana :

Goalkeepers: Fatau Dauda (Orlando Pirates, Afrika ta Kudu), Adam Kwarasey (Stromgodset, Norway), Richard Kingson (Doxa Katokopias, Cyprus)

Defenders: Samuel Inkoom (Dnipro, Ukraine), Daniel Opare (Standard Liege, Belgium), David Addy (Vitoria Guimaraes, Portugal), Baba Abdul Rahman (Greuther Furth Jamus), John Boye (Rennes, France), Jerry Akaminko (Eskisehirspor, Turkiya), Rashid Sumaila (Mamelodi Sundowns, Afrika ta Kudu), Mohammed Awal (Maritzburg United, Afrika ta Kudu)

Midfielders: Michael Essien (Chelsea, Ingila), Emmanuel Frimpong (Arsenal, Ingila) Sulley Muntari (AC Milan, Italiya), Kwadwo Asamoah (Juventus, Italiya), Emmanuel Agyemang Badu (Udinese, Italiya), Kevin Prince Boateng (Schalke, Jamus), Albert Adomah (Middlesbrough, Ingila), Mubarak Wakaso (Rubin Kazan, Rasha), Christian Atsu (Vitesse Arnhem, Holland), Andre Ayew (Marseille, Faransa)

Strikers: Asamoah Gyan (Al Ain, UAE), Abdul Majeed Waris (Spartak Moscow, Rasha), Jordan Ayew (Marseille, Faransa), Mahatma Otoo (Sogndal, Norway).

Karin bayani