Har yanzu da saurana —Drogba

Image caption Drogba ya ce har yanzu yana kan ganiyarsa

Didier Drogba ya bayyana cewa ya koma kungiyar Galatasaray a watan Janairu ne saboda yana so ya kara buga wasa a Gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Drogba, dan kasar Ivory Coast, ya bar Chelsea ne zuwa China a shekarar 2012 bayan kungiyar ta lashe Kofin Zakarun Turai amma ya koma wasa nahiyar Turai a watan Janairu.

Galatasaray ta kai wasan kusa da kusa dana karshe a kakar wasa ta bara.

Drogba dai ya kagu ya nuna cewa har yanzu zai iya taka rawa a manyan wasanni.

Ya ce, ''Na dawo Galatasaray domin kara daukar Kofin Zakarun Turai da na dauka a Chelsea, na kuma nuna cewa har yanzu da saurana''.

Yau Galatasaray take karbar bakuncin Juventus a Gasar cin Kofin Zakaru na nahiyar Turai.

Karin bayani