Ba zan koma Manchester United ba —Ferguson

Image caption Ferguson ya ce Moyes zai iya jagorancin United

Tsohon kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson, ya ce ba zai koma kungiyar domin jagorantarta ba.

Kungiyar ce ta 12 a teburin Gasar Premier a karkashin jagorancin David Moyes, wanda ya karbi jagorancinta bayan Ferguson ya yi ritaya a watan Mayu.

Ferguson ya ce, "Bani da sha'awar komawa kungiyar, don bana son na wahalar da kaina. United tana hannun mutumin da zai iya gudanar da ita da kyau. David zai iya gudanar da ita. Mutum ne mai kwazo''.

Tsohon kocin kungiyar, mai shekaru 71 a duniya, ya kara da cewa Roman Abramovich ya bukace shi ya zama kocin Chelsea lokacin da ya sayi kungiyar a shekarar 2003.

Ya ce, "Abramovic ya sanya wani ya tunkare ni game da yiwuwar jagorancin kungiyar lokacin da suka saye ta, amma na ce bana so''.

Karin bayani