An tsawaita dakatarwar da aka yi wa Klopp

Image caption Klopp zai kasance cikin 'yan kallo lokacin da Borussia Dortmund za ta fafata da Arsenal

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp, zai kasance a cikin 'yan kallo lokacin da kungiyar tasa za ta kara da Arsenal a wasan cin Kofin Zakarun Turai, bayan da aka tsawaita haramcin da aka yi masa na shiga fili da wasa guda.

Tun farko dai hukumar kwallon kafa ta Turai, wato Uefa, ta dakatar da kocin dan shekaru 46 da haihuwa ne wasa daya, bayan da sukayi sa in sa da alkalin wasa mai jiran ko ta kwana, a wasan da Napoli ta sami nasara a kansu da ci 2-1 a watan da ya gabata.

Sai dai kuma bayan hukumar kwallon ta Turai ta sake nazari a kan lamarin ranar 2 ga watan Oktoba, ta yanke shawarar tsawaita haramcin; wato ke nan ba zai shiga fili ba yayin wasan da za a yi a filin wasa na Emirates.

Dortmund ta casa Olympique de Marseille da ci 3-0 a filin wasa na Signal Iduna Park ranar Talata, za kuma ta kara da Arsenal ta a filin Emirate ranar 22 ga watan Oktoba.