Zan so sanin sunayen 'yan wasa — Mancini

Roberto Mancini Galatasaray
Image caption Babu wani abu muhimmi da zan iya a kwana biyu, amma yanzu zan nemi sanin sunan 'yan wasa

Kocin Galatasaray Roberto Mancini, zai nemi sanin sunan 'yan wasansa bayan da aka tashi 2-2, a wasansu da Juventus a gasar kofin zakarun Turai.

Tsohon kocin Manchester City, Mancini ya karbi kungiyar bayan ya rage kwana biyu su kara a garin Turin.

Mancini wanda ya karbi ragamar koci a hannun Fatih Terim da aka sallama a satin da ya gabata yace "a yanzu ban san sunan 'yan wasa na ba."

Mancini yace ya yi mamakin yanda Didier Drogba mai shekaru 35, wanda ya fara jefa kwallo daga baya a ka farke, ke taka leda.