An haramtawa Sessegnon tuka mota

Image caption Stephane Sessegnon

An haramtawa dan kwallon West Brom, Stephane Sessegnon tuka mota na tsawon watanni 20 saboda laifin tuka mota bayan ya sha giya.

Dan wasan mai shekaru 29, ya koma West Brom ne daga Sunderland a watan da ya wuce, kuma an tsare shi ne a birnin Newcastle bayan wasan da suka yi.

Wata kotu a Newcastle ta same shi da laifin sharara gudu a mota fiye da kima a ranar 27 ga watan Agusta.

Dan wasan na kasar Jamhuriyar Benin ya amsa laifinsa.

An kuma ci tararsa fan 7,605 .

Karin bayani