Wenger ya soki Wilshere kan sigari

Image caption Jack Wilshere

Manajan Arsenal Arsene Wenger, ya bayyana cewar ba zai yadda da dabi'ar Jack Wilshere ta shan sigari ba.

A cewar kocin, zai fuskanci Wilshere gaba da gaba don su tattauna batun.

A ranar Alhamis da safe ne aka dauki hoton Wilshere yana fitowa daga wata mashaya a London yana bukan sigari.

Lamarin ya faru ne a daren ranar da Arsenal ta lallasa Napoli daci biyu da nema, amma ba a soma wasan da Wilshere ba.

Wenger yace "sam ban yadda da wannan dabi'ar ba, ban san abinda ya faru ba, amma zan tattauna dashi".

Karin bayani