Ba zan sayar da Lazio ba —Lotito

Latito lazio President
Image caption Tun lokacin dana zama shugaban lazio ban taba tunanin sayar da kungiyar ba

Shugaban kungiyar Lazio Claudio Lotito, ya ce ba zai sayar da kungiyar ba, duk da tayin da masu sayen hannun jarin kungiyar ke yi.

Tuni aka sayar da Roma, yayin da shugaban Inter Massimo Morrati, yake kokarin sayar da kungiyar ga dan kasar Indonesia Erick Thohir, gasar kwallo a Italy, ita ma ta bi sahun sauran wasannin Turai.

Lotito ya jaddada cewar ba zai bi sawun sauran kungiyoyin ba, kuma ba zai yi wasa da jarinsa da ya sa a kungiyar ba.

Mai shekarun haihuwa 56 ya mallaki kungiyar a shekara ta 2004, ko da yake ana matsa masa da ya canja salon juya kungiyar, amma ya ce zai ci gaba da jagorantar kungiyar.