Na kusa na ajiye Hart — Pellegrini

 Joe Hart Manchester City
Image caption Pellegrini na tuna nin sauya mai tsaron raga Hart

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini, ya so ya ajiye mai tsaron ragar England Joe Hart, a karawar da suka yi da Everton.

Hart, da ake zargin ya yi kura-kurai a satuttukan baya, an zura masa kwallo ta hannun Romelu Lukaku kafin daga baya su lashe wasa da ci 3-1.

Kwallon da aka zura masa ta sa shakku game da tashen da mai tsaron ragar ke yi .

Pellegrini ya ce "ya kamata a samu amincewata da ta 'yan wasa da magoya bayan kungiyar"