Spain ta gayyaci Michu

Image caption Michu

A karon farko Spain ta gayyaci dan kwallon Swansea City Michu, don buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya tsakaninta da Belarus da kuma Georgia.

Ya maye gurbin David Villa na Atletico Madrid wanda ya samu rauni a wasansu da Celta Vigo.

Michu ya koma Swansea a kan fan miliyan2 a shekera ta 2012 inda ya zira kwallaye 22 a kakar wasan da ta wuce.

Tawagar Spain:

Masu tsaron gida: Iker Casillas (Real Madrid), Victor Valdes (Barcelona), Pepe Reina (Napoli).

'Yan baya: Alvaro Arbeloa (Real Madrid), Sergio Ramos (Real Madrid), Gerard Pique (Barcelona), Inigo Martinez (Real Sociedad), Nacho Monreal (Arsenal), Juanfran (Atletico Madrid), Alberto Moreno (Sevilla).

'Yan tsakiya: Andres Iniesta (Barcelona), Isco (Real Madrid), Koke (Atletico Madrid), Xavi (Barcelona), Mario Suarez (Atletico Madrid), Sergio Busquets (Barcelona), Cesc Fabregas (Barcelona), Juan Mata (Chelsea), David Silva (Manchester City).

'Yan gaba: Jesus Navas (Manchester City), Alvaro Negredo (Manchester City), Pedro (Barcelona), Michu (Swansea).

Karin bayani