Herve Renard ya bar kocin Zambia

Bernard Herve Zambia
Image caption Hukumar kwallon kafa ta Zambia ce ta bada sanarwa ajiye aikin da kocin yayi

Tsohon Kocin Zambia Herve Renard ya bar kasar, zai koma kocin kungiyar Sochaux ta Faransa.

Renard ya fara kocin Zambia a shekara ta 2011, ya kuma jagoranci kasar ta lashe kofin nahiyar Africa, watanni hudu da kama aikin sa.

Zambia ta maye gurbin Herve Renard da Patrice Beaumella a matsayin kocin riko.

Beaumella mataimaki Renard, zai fara aiki a wasan sada zumunci da Zambia za ta kara da Brazil ranar 15 ga watan Oktoba a Beijin.