Ni ba mashayin taba ba ne —Wilshere

Jack Wilshere Arsenal
Image caption "Wenger ya sani a wasan da muka kara da West Brom, kuma na wanke kaina"

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshere yace shi ba kabusu bane, duk da an dauki hotonsa a gidan rawa yana busa taba.

Kocin Arsenal ya soki dan wasan mai shekarun haihuwa 21 a kan abin da ya faru, amma ya saka shi a wasan da suka yi da West Brom wanda aka tashi ci 1-1, ranar Lahadi data gabata.

Wilshere ya shedawa shafin internet na Arsenal ce wa "nayi kuskure.'Yan wasa su kanyi kuskure"

Wilshare, zai buga wasan da England zata kara da Montenegro da Poland a wasan neman shiga kofin duniya, ya kuma farke wa Arsenal kwallo daga yadi na 20 a filin wasa na The Hawthorns.