Ghana na son sauyi kan wasanta Masar

Image caption Ghana ta ce tana faragaba game da tsaron 'yan wasanta.

Hukumar kwallon kafa ta Ghana ta bukaci FIFA ta sauya wajen da za ta buga wasanta da Masar saboda tashin hankali.

Kungiyar ta nuna damuwarta ne bayan an kashe mutane da dama a karshen mako a gwabzawar baya-bayan nan da aka yi a birnin Alkahira tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan hambararren shugaban kasar, Mohammed Morsi.

Za dai a buga wasan ne a Alkahira ranar Talata 19 ga watan Nuwamba.

A wata wasika da ta wallafa a shafinta na intanet, hukumar kwallon kafar ta Ghana ta ce,"Mun bukaci a sauya wajen ne saboda yanayin tsaro a kasar Masar na dada tabarbarewa''.

Hukumar ta kara da cewa rikicin da ke faruwa a Masar ba shi da alamar karewa, don haka ne take nuna damuwa game da irin halin da 'yan wasa da jami'anta za su iya fadawa a ciki idan suka je Masar.

FIFA ta ce ta karbi korafin da Ghana ta yi, tana mai cewa tana duba yadda al'amura ke faruwa a Masar amma ba ta bai wa Ghana tabbacin sauya wajen wasan ba.

Karin bayani