Poyet ya zama sabon kocin Sunderland

Image caption Gus Poyet

An nada tsohon kocin Brighton Gus Poyet a matsayin sabon kocin Sunderland a yarjejeniyar shekaru biyu.

Kungiyar wacce take karshe a kan jadawalin gasar Premier ta Ingila ta kori Paolo Di Canio bayan jagorantar kulob din a wasanni 13.

Poyet ya shaidawa shafin intanet na Sunderland cewar " na zaku in soma aiki da tare da 'yan wasa"

Ya koma Sunderland tare da sauran mataimakansa a Brighton wato Mauricio Taricco da Charlie Oatway.

Tsohon dan kwallon Uruguay din ya kasance kocin Sunderland na shida a cikin shekaru biyar.

Karin bayani