Shugaban Kamaru ya lallashi Eto'o

Image caption Samuel Etoo

Shugaban Kamaru Paul Biya, ya lallashi Samuel Eto'o ya sauya hukuncin sa na daina bugawa kasar kwallo.

Eto'o dan kwallonChelsea, ya tattauna da wakilan shugaban kasar, don sanin inda yasa alkiblar kwallon sa.

Eto'o ya amince zai dawo bugawa Kamaru kwallo, bayan sun kammala taron, zai kuma tafi Faransa don haduwa da sauran tawagar 'yan wasa da suke atisaye domin karawa da Tunisiya a wasan shiga kofin duniya

Dan kwallon m,ai shekaru 32, ya sanar wa abokan kwallon sa cewa ya daina bugawa Kamaru kwallo, lokacin da suka sami nasara akanLibyaa wasan neman gurbin zuwa gasar kofin Duniya.

Karin bayani