Ingila na bukatar 'yan kasa- Wilshere

Image caption Jack Wilshere

Dan kwallon Arsenal Jack Wilshere ya ce 'yan Ingila ne kadai zasu buga wa kasar Tamaula.

Dan kwallon United Adnan Januzaj zai iya bugawa Ingila wasa, idan ya cika shekaru biyar na zama a kasar a ka'idojin FIFA, tun da har yanzu bai bugawa wata kasa kwallo ba.

Januzaj mai shekaru 18, yana da damar zabar kasar da zai bugawa kwallo, tsakanin Belgium da Serbiya da Albaniya da kuma Turkiya.

Wilshere ya kara da cewa "Domin ka zauna shekaru biyar a Ingila, baka zama dan kasa ba."

"Muna da 'yan wasa da yawa dake wakiltar Ingila, wanda iyayen su ne suka dawo da zama a nan."

Karin bayani