Jordi Alba zai yi jinyar makonni 6

Image caption Jordi Alba da Ramos na Spain

Dan kwallon Barcelona Jordi Alba zai yi jinyar makonni shida, sakamakon rauni da ya ji a cinyarsa.

Dan kwallon mai 24 ya soma murmurewa daga wani raunin kafin yaji sabon rauni.

Barca ta na matsayi na daya a teburin La-Liga, bayan da ta lashe wasanni takwas a jere, tana kuma da banbancin yawan kwallaye tsakaninta da Atletico Madrid.

Kawo 'yan kwallon Barcelona biyu Javier Mascherano, mai shekaru 29, da Carlos Puyol, mai shekaru 35, sun warke daga raunin da suka samu.

Mascherano ya sami rauni a wasan da suka lashe Real Sociedad daci 4-1, shi kuwa Puyol ya fara jinya tun a Maris da gwiwarsa ta hana masa kwallo.

Karin bayani