'Ingila ta cire ran daukar kofin duniya'

Image caption Tsohon kocin Ingila, Glenn Hoddle

Tsohon kocin Ingila Glenn Hoddle yace kada Ingila tasa ran daukar kofin duniya da za ayi a Brazil shekara ta 2014, amma su tara a shekaru masu zuwa.

Hoddles ya bayyana haka a taron hukumar kwallon kafa ta Ingila, lokacin da aka tattauna a kan hanyoyin ci gaban Ingila a wasan kwallon kafa.

Ya shaidawa BBC cewa "A bune mai wuya kayi tunanin Ingila zata je Brazil ta lashe kofin duniya."

"Da farko mu samu gurbin zuwa gasar kofin duniya, matasan 'yan kwallon mu su sami kwarewa, nan da shekaru biyu masu zuwa sai mu fara sa ran kofin nahiyar Turai."

Shugaban hukumar kwallon kafa na Ingila Greg Dyke, shima ya ce Ingila tasa ran tabuka rawa a gasar kofin duniya na 2022.