Ban aika wa Redkapp sako ba - Gerrard

Image caption Kyaftin din Ingila, Steven Gerrard

Steven Gerrard ya ce bai shaidawa Harry Redknapp ya goyi da bayan a nada shi kocin Ingila ba.

Kocin QPR Rednapp ya rubuta a tarihinsa da ake wallafawa a mujallar Daily Mail, cewa manyan 'yan wasan Ingila har da kaftin din Ingila Steven Gerard sun tura masa sakwan wayar sadarwa suna mara masa baya.

Gerrard mai shekaru 33, ya ce bashi da lambar salular Rednapp, saboda haka bai taba tura masa sako ba.

Daga baya Ingila ta dauki Roy Hodgson a sabon kocinta a watan Mayu cikin shekara ta 2012.

Gerrad yace "dan sa Jamie aboki nane, kuma na gaya masa cewa ina yiwa mahaifinsa fatan alheri, idan an dauke shi aiki zamu mara masa baya

Gerrad zai bugawa Ingila wasa na 106 a wasan da zasu kara da Montenegro a wasan neman shiga kofin duniya.

Karin bayani