Juventus na kokarin sayar da Pogba

Image caption Juventus za ta sayar da Pogba ne saboda ba ta da kudi

Juventus ta ce za ta sayar da, Paul Pogba, saboda karancin kudi da take fama a da shi.

Shugaban kungiyar, Andrea Agnelli, ya ce abu ne mai wahala a ki sayar da Pogba, tsohon dan wasan Manchester United mai shekaru 20, idan har wata kungiya ta taya shi da daraja.

Ya kara da cewa "abu ne mai wahala mu rike dan wasan domin ba mu da kudin da za mu rika biyansa"

Pogba ya koma Juventus a watan Yuli a shekara ta 2012, bayan ya ki amincewa da yarjejeniyar da United ta nemi ya yi, ya buga wasanni 47 ya jefa kwallaye 7.

Karin bayani