Ana sayar da wasanni a gasar La Liga

Image caption Akwai zaratan 'yan wasa a gasar La Liga ta Spain

Shugaban shirya gasar wasanni na kasar Spain Javier Tebas yace ana saida akalla wasanni takwas a cikin manyan matakan wasannin Kasar Spain biyu a kowanne kakar wasanni.

Da yake bayani ta cikin shirin wasannin na gidan rediyon BBC, Tebas ya kuma yi kira da'a dakatar da 'yan wasan da suke sayar da wasa.

"Yace tsakanin matakan farko dana biyu na wasannin, kimanin wasanni 8 zuwa10 ne akayi magudi a cikinsu"

"Yace idan ba'a gaggauta kawadda matsalar ba, to kuwa zata ci gaba da yin illa.

Tebas wanda shine shugaban gasar wasanni na kasar Spain, ya kuma shedawa shugabanni a Taron kwallon kafar da aka gudanar a birnin Landan cewa ya yi imanin babbar matsalar na fitowa ne daga wasu mutane dake kitsa ta a kasashen duniya.