Sharhi Kai Tsaye a kan wasan Ethiopia da Nigeria

Sharhi kai tsaye a kan wasan Ethiopia da Nigeria

Latsa nan don sabunta shafin.

16:30: Karshen wannan sharhin kenan na wasa tsakanin Nigeria da Ethiopia wanda Super Eagles ta doke Waliya Antelopes daci 2 da 1.

16:25: Sauran wasanni na Afrika: Kamaru zata kara da Tunisia, sai kuma a ranar Talata Ghana ta hadu da Masar a birnin Kumasi.

16:21: 'Yan Ethiopia zasu ciji yatsa saboda rashin nasara a cikin gidansu.

16:18: Mataimakin kocin Super Eagles, Daniel Amokachi ya ce " Dama wasan bazai zo da sauki ba kuma a zangon farko sun wahalar damu. Daga karshe mun samu nasara. Amma akwai sauran wasa idan sun zo Calabar".

Ra'ayoyi:

BBC Hausa Facebook:

"Gabadai Super Eagles wani abu sai mun je Brazil",Hassan Adamu Dukku. "Raina kama ka ga gayya ...Super Eagles har yanzu da sauran rina a kaba domin a Brazil",Mohammed Dan India,

Twitter @bbchausa: "Ai wannan ya nuna cewa kofi namu ne idan mun kai gasa a Brazil", @ mrabduul, GuY Man: @bbchausa

16:11: Akwai bukatarNigeria za yi galaba a kan Ethiopia a wasan da za a buga a Calabar, don tabbatar da gurbinta na zuwa gasar da za a buga a Brazil.

16:07: Nan gaba a yau, Kamaru za ta san makomarta bayan ta hadu da Tunisia a Yaounde.

BBC Hausa Facebook: "Wasa ya yi kyau, da kyar na sha ya fi da kyar aka kama ni", Hamidan Yusuf.

"An yi wa Ethiopia fasha amma ba komai zuwa marakana ba shine daukar kofi ba",Jamideen Idris Adam.

16:03: 'Yan wasan Ethiopia 5 sun karbi katin gargadi a wasan da aka kammala; Tesfaye Seyoum, Girma Adane, Behailu Assefa, Addis hintsa, Aynalem Hailu.

Ra'ayoyi:

Twitter @bbchausa:Dama ai sama ta yiwa yaro nisa kuma linzami yafi karfin bakin kaza super eagles kunnuna cewa ruwa ba tsaran kwando bane. Abba Geidam

BBCHausafacebook: "Dama Nigeria tafi karfin Ethiopia up 9ja", Lirwanu Aminu Gamawa.

15:58: Sakamakon wannan wasan ya nuna cewar Nigeria za ta wasa na biyu da karfinta.

15:57: A watan Nuwamba, Nigeria za ta dauki bakuncin Ethiopia a birnin Calabar.

15:55: An tashi wasa, Ethiopia (Behailu ASSEFA 57') 1 Nigeria (Emmanuel EMENIKE 67', 90' PEN) 2.

15:54: Nigeria sun karbi wasan sai raba kwallo suke suna kuma kai zafafan hare -hare

Image caption Emenike na murnar kwallon daya ciwa Nigeria

15:53: Kwallon da Amuneke yaci itace ta 20 da Nigeria ta zurawa Ethiopia kwallo

15:51: Emmanuel Emenike ya ciwa Nigeria kwallo na biyu.

15:49: Ethiopia 1 Nigeria 2

Goal! Goal!! Goal!!! Goal!!!!

15:48: Nigeria za ta buga fenariti

Ra'ayoyi:

BBC Hausa Facebook: "Kai Habasha ba ku san Super Eagles ba; ko kun bi a hankali, ko ba haba ba sai mun casa ku. Up 9ja" Abbas Isah Baffari Dango.

"Up Ethiopia", Musa Muhammad Ma'aji.

Ku biyo mu a shafinmu na bbchausafacebook, da kuma @bbchausa wato a twitter don bayyana ra'ayoyinku.

15:47: Sauran mintuna biyu a tashi wasa, Ethiopia (Assefa 56') 1 Nigeria (Emenike 67') 1

15:45: An baiwa dan Ethiopia, Addis Hintsa katin gargadi.

15:44: 'Yan kallon Ethiopia sai tagumi suke, sun san idan wasa ya tashi haka da sauran aiki.

15:42: Oboabona ya taimaki Nigeria da Salahdin Ahmed ya kara shigar da Ethiopia gaba.

15:41: Magoya bayan Ethiopia suna cikin fargaba saboda Nigeria na shafa Waliya Antelopes

15:38: Ethiopia (Assefa 56') 1 Nigeria (Emenike 67') 1

15:36: Ahmed Musa ya gwada gola a kurkusa, amma sai kwallon ta daki turke.

1534: Ahmed Musa ya fadi kasa a cikin yadi na 18 a gidan Ethiopia amma alkalin wasa yaki bada bugun fenariti.

15:30: Wasa na kara zafi a tsakanin Ethiopia da Nigeria a Addis Ababa tunda Super Eagles suka farke.

Ra'ayi: BBC Hausa Facebook: "Yakamata Nigeria su canza wasansu", Akilu Sani.

15:26: Ethiopia 1 Nigeria 1, Emmanuel Emenike ya ciwa Nigeria kwallo.

Goal! Goal!! Goal!!! Goal!!!!

15:25: Ethiopia 1 Nigeria 0 (65')

15:24: Nigeria Brown Ideye ya canji Victor Moses.

15:23: Canji a bangaren Ethiopia, Adane Girma ya fita, sai kuma Omod OKWURY

15:22: Victor Moses ya barar da kwallo daga shi sai gola.

15:21: 'Yan Ethiopia na cike da farin cikin saboda kwallon da suka zira a ragar Super Eagles.

Ra'ayoyinku:

BBC HausaFacebook: Kamal Mu'awiya Madobi, "anya 'yan wasan Najeriya za mu iya kuwa?

Twitter @bbchausa: Bashir Ahmad " 'Yan Nijeriya sama da miliyan 150 suna kanku 'yan Super Eagles, burin mu ku casa Habasha, domin ku faranta mana rai".

Ku biyo mu a shafinmu na bbchausafacebook, da kuma @bbchausa wato a twitter don bayyana ra'ayoyinku.

15:17: Dan wasan Ethiopia, Behailu ASSEFA ya zira kwallo a ragar Nigeria. Wasa sabon aji!

15:16: Ethiopia 1 Nigeria 0

Goal! Goal!! Goal!!! Goal!!!!

15:15: Katin gargadi a kan dan wasan Ethiopia, Girma Adane.

15:14: Enyeama ya ceci Nigeria a hannun Salahdin Ahmed inda ya fito daga cikin yadi na 18 ya more kwallon.

Image caption Victor Moses ya kai hari amma bai samu zira kwallo ba.

15:11: Ethiopia 0 Nigeria 0 (53')

15:09: Ethiopia bata taba zuwa gasar cin kofin duniya ba, Nigeria ta halarci gasar sau hudu wato 1994,1998,2002,2010.

BBC Hausa facebook : Nigeria sai kun yi da gaske.Allah bamu sa'a, Murtala Ibrahim.

Ra'ayi:Twitter @bbchausa:

"Kwallo dai sa'a ce amma ya kamata Najeriya mu kara zage damtse dan kuwa da alamu za ta bare damu". Abba Geidam

15:05: An dawo hutun rabin lokaci, Ethiopia 0 Nigeria 0.

15:03: A bangaren Ethiopia, masu zaman benci sune; Mogos TADESE,Birhanu BOGALE, Omod OKWURY .

15:00: A masu jiran kota kwana a Nigeria akwai Victor OBINNA, Emmanuel Sunday, Nosa IGIEBO, wadanda za a iya shigo dasu bayan ana dawo hutun rabin lokaci.

14:56: Muhammed Abdu na BBC Hausa ya ce Ethiopia sun sami dama da yawa na zira kwallo a raga amma basu da sa a. Sun kwaso kwana sau biyu, Nigeria ma ta samu kwana biyu dan wasan Ethiopia Salahdin Ahmed ya matsawa Nigeria musamman ta bangaren hannun hagu wajen ya zama rariya matuka.

14:54:Twitter @bbchausa: "Super Eagles kar ku ba mu kunya fa, kuma kada ku manta cewa kofin Afirka ma a hannunku ya ke". Abdallah Binjaajsz

Ku biyo mu a shafinmu na bbchausafacebook, da kuma @bbchausa wato a twitter don bayyana ra'ayoyinku.

14:51: Sakamakon wasannin da aka buga a ranar Asabar;Burkina Faso 3 - 2 Algeria Cote d'Ivoire 3 - 1 Senegal

14:48: Hutun rabin lokaci. Ethiopia 0 Nigeria 0

14:47: Salahdin na Ethiopia ya barar da kwallo.

14:45: Vincent Enyeama ya ceci Nigeria, saboda saura kiris kwallo ta shiga amma ya dunkulleta.

14:44: Ana gabda tafiya hutun rabin lokaci, 'yan Ethiopia na matsawa 'yan Nigeria amma kuma babu ci kawo yanzu.

Image caption Wasan da aka buga a Afrika ta Kudu, inda Nigeria ta doke Ethiopia daci 2 da 0.

14:41: Ethiopia 0 Nigeria 0

14:40: Nigeria tana matsayi na 36 a jadawalin FIFA, matsayi ta 4 a Africa. Ethiopia tana matsayi na 93 a FIFA tana matsayi na 25 a Africa.

14:38: Ethiopia na shafa 'yan Nigeria, amma kuma bisa dukkan alamu 'yan Ethiopia ba suda sa'a.

1436: Adane ya gwada golan Nigeria daga nesa, amma kwallon ta fita zuwa bugun gida.

14:30 :Ethiopia 0 Nigeria 0

Ra'ayoyi:

BBC Hausa facebook : "To Super Eagles idanun 'yan Nigeria suna kanku. Ku taka leda sosai". Usman Gashua, Yobe.

BBC Hausa facebook : "Ba matsala ta ba ce ko Nigeria ta sha Ethopia, Nigeria ko kuma Ethopia ta sha , ko ohoo..,.!" Yusuf Bala.

Ku biyo mu a shafinmu na bbchausafacebook, da kuma @bbchausa wato a twitter don bayyana ra'ayoyinku.

Image caption Daruruwan magoya bayan Nigeria sun halarci wasan

14:24:Salahdin Ahmed ya buga kwallon cikin ragar Nigeria, amma Oboabona ya fitar da kwallon bayan ta wuce Enyeama

14:23: Girma ADANE ya gwada Enyeama,amma golan Super Eagles ya kama

14:22: Dan Nigeria, Oduamadi ya barar da kwallo daga shi sai gola.

14:21: Ethiopia 0 Nigeria 0

14:20: Golan Ethiopia Tassew ya yi kuskure, sauran kadan Nigeria ta shiga gaba.

14:19: An baiwa dan wasa Ethiopia, Tesfaye SEYOUM katin gargadi daya kayar da Onazi na Nigeria.

14:17: A tawagar Ethiopia, 'yan wasa hudu ne kawai ke taka leda a kasashen waje.

14:14: Sunday Mba na Nigeria yana kan benci

14:12: Dan wasan Ethiopia mai zira kwallo, Getaneh Kebede Gibeto baya wasa saboda raunin daya samu a gwiwarsa.

14:10: An shafe mintuna 10 ana karawa, Ethiopia 0 Nigeria 0

14:06: A watan Junairun 2013, Nigeria ta doke Ethiopia daci 2 da 0 a gasar cin kofin kwallon Afrika da aka buga a Afrika ta Kudu

14:02: Ethiopia sun kai hari amma golan Nigeria Vincent Enyeama ya fitar da kwallon zuwa bugun kusurwa.

14:00: An soma wasan a Addis Ababa: Ethiopia 0 Nigeria 0

Image caption Keshi da Amokachi suna taken Nigeria

13:54:Ethiopia: Ethiopia: Jemal TASSEW (GK), Degu DEBEBE, Abebaw BUTAKO, Aynalem HAILU, Salahdin AHMED , Asrat GOBENA, Menyahel TESHOME, Tesfaye SEYOUM, Shemeles BEKELE, Girma ADANE, Behailu ASSEFA.

13:52 :Nigeria: Vincent ENYEAMA,Ahmed MUSA,Azubuike EGWUEKWE, Efe AMBROSE, Emmanuel EMENIKE,Godfrey OBOABONA,John Obi MIKEL, Nnamdi ODUAMADI,Ogenyi ONAZI,Uwa ECHIEJILE, Victor MOSES.

Image caption Kocin Waliya Antelopes, Sewnet Bishaw ya ce zasu baiwa Nigeria mamaki

13:49:Sun kara a karawa ta hadu, Yuli 24,1993 a wasa na biyu na neman gurbin shiga kofin nahiyar Africa, Nigeria ta zura kwallaye 6-0. Rasheedi Yakini ya zira kwallaye 3.

13:47: Karawa ta uku itace wacce Ethiopia ta samu nasara daci 1-0 a Addis Ababa 1993.

13:45:Sun fara karawa a 1982 a gasar kofin Nahiyar Afrika a Libya, Nigeria ta samu nasara daci 3-0.

Karawa ta biyu a wasan sada zumunci suka hadu a 1993 a Addis Ababa, Nigeria ta samu nasar da ci 1-0.

Image caption Kocin Super Eagles Stephen Keshi ya bukaci 'yan wasa su yi kwazo

13:39:Nigeria ta zira kwallaye 18 a ragar Ethiopia, ita kuwa Ethiopia ta zira kwallaye 3 kacal.

13:36:Nigeria ta samu nasara a wasanni biyar a yayinda Ethiopia ta samu nasara a wasa daya sai aka tashi canjaras a wasa daya.

13:34: A tarihi Ethiopia da Nigeria sun kara sau bakwai

1330: Barkanmu da warhaka, sashin Hausa na BBC zai soma gabatar muku da sharhi kai tsaye a kan wasan Ethiopia da Nigeria wanda za a buga a birnin Addis Ababa.