Nigeria ta doke Ethiopia

Emanuel Emeneke
Image caption Emannuel Emeneke shine ya zura kwallaye biyu

Nigeria tasha da kyar a Addis Ababa, bayan data zira wa Ethiopia kwallaye biyu da daya a wasan farko na neman gurbin shiga kofin Duniya.

Ethiopia tun farko ta matsawa Nigeria da kai hare-hare, sai a minti na 56 maim tsaron ragar Nigeria Vincent Enyeama ya kama kwallo yana cikin raga, a bugun da Behailu Assefa ya bugo kwallo.

Duk da Nigeria bata taka kwallo ba, ta farke kwallo ta hannun Emmanuel Emenike.

Emmanuel Emenike ya samowa Nigeria dukan daga kai sai mai tsaron raga, ya buga ya kuma zura kwallo.