Tunisia da kamaru sun tashi babu ci

Tunisia vs Camaru
Image caption Tunisia da Kamaru sun sami damar zura kwallaye

Tunisia da Kamaru sun barar da damar da suka samu a wasan farko na neman gurbin shiga kofin duniya inda suka tashi babu ci a filin wasa na Rades dake Tunis.

Tunisia ta kai hare-hare zafafa, amma golan Kamaru Charles Itandje ya sa kaimi bai yadda kwallo ta shiga raga ba.

Saura kiris Kamaru ta jefa kwallo a ragar Tunisia, amma dama ta kwace mata lokacin da dan wasanta Pierre Webo ya hambari kwallo da kirjinsa, kuma tsakaninta da fadawa raga yadi biyar ya rage.

Kamaru ta kusan samun Fenariti daf da tashi lokacin da Sameh Derbaly ya sa hannu.

Za su kara a wasa na biyu, inda za a raba gardama ranar 17 ga watan Nuwamba a Yaounden Kamaru.