Raunin Boateng ba karya ba ne —Nyantakyi

Prince Boateng Ghana
Image caption Sau tari yana samun matsala a gwiwarsa

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana, Kwesi Nyantakyi, ya kare Kevin-Prince Boateng daga sukar da ake yi masa saboda janyewa daga tawagar Black Stars.

Magoya bayan Ghana na zargin Boateng, dan kwallon Schalke, da lambon rauni, saboda kada ya buga zagaye na farko na karawar da Ghana za ta yi da Masar a wasan neman shiga kofin duniya.

Wasu daga cikin magoya bayan kasar ta Ghana dai sun yi ikirarin cewa Boateng ba shi da kishin kasa.

Sai dai Nyantakyi ya ce "Kowanne dan kwallo zai yi so ya halarci Gasar cin Kofin Duniya; wannan ne kuma matakin zuwa Gasara. Don haka Kevin yana burin ina ma yana nan".

Ya kuma kara da cewa babu dalilin da zai sa a yi tunanin cewa raunin da Kevin ya yi bai kai yadda ake fada ba.